Rundunar sojin ruwan Najeriya ta ƙalubalanci tsohon jagoran masu fafutika na yankin Neja
Delta, Mujahid Asari Dokubo da ya bayyana sunayen jami’an da ke satar ɗanyen mai.
A ranar Juma’a ne Asari Dokubo ya yi zargin cewa akwai hannun sojojin Najeriya na ruwa a yawancin laifukan satar mai da ake samu a yankin Neja-Delta.
Dokuba ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da manema labarai na fadar shugaban ƙasa bayan ganawarsa da shugaba Bola Tinubu.
Sai dai yayin da yake mayar da martani, mai magana da yawun rundunar sojin ruwan Najeriya, Commodore Adedotun Ayo-Vaughan, ya bayyana zargin a matsayin maganar da babu gaskiya a cikinta.
Ya ce ɓarayin mai sun fusata ne saboda sojojin ruwan Najeriya da ɗaukacin sojojin na ci gaba da
hana su hanyoyin da za su yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta hanyar wani shiri na dakatar
da ayyukan ɓarayi.
Ya ci gaba da cewa rundunar sojin ruwa tare da hadin guiwar masu ruwa da tsaki za su ci gaba
da hana ɓarayin danyen mai hanyoyin yin zagon kasa ga tattalin arzikin Najeriya.
A yayin ganawarsa da ‘Yan jaridu Ayo- Vaughan,ya ce “Ya kamata Dokubo ya kawo sunayen sojojin da ya ke zargi.