Olusegun Obasanjo yayi magana kan tazarcen da ya so ya yi karo nauku wanda bai yi nasara

Tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya yi magana kan tazarcen da ya so ya yi karo na
uku wanda bai yi nasara ba lokacin yana kan mulkin ƙasar nan a karo na biyu.

Idan ba a manta ba a shekarar 2006, an kai wani kuɗiri gaban majalisar tarayya domin yi wa kundin tsarin mulkin shekarar 1999 gyara da ƙara wa’adin mulki, ƙudirin da aka ƙi amincewa da shi.

Obasanjo ya bayyana cewa akwai hannun wasu gwamnonin jihohi a cikin tazarcen karo na uku saboda suna son su yi hakan a jihohinsu.

Da ya ke magana a yayin tattaunawa da wani gogaggen ɗan jarida, Chude Jideonwo, tsohon shugaban ƙasar ya bayyana cewa wasu gwamnonin sun so ƙara wa’adin mulkinsu da shekara huɗu.

Da yake magana kan zarge-zargen salwantar da dukiyar ƙasa da ake masa, Obasanjo ya bayyana cewa ya ƙware ne a wajen samar da kuɗi ba salwantar da su ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *