Jonathan: EFCC ba ta taba gayyata ta ba

Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan ya ce Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasar ta’annati ba ta taba gayyatarsa ba.

Jonathan na wannan furuci ne a matsayin musanta ikirarin da mawakin nan Femi Kuti ya yi a kansa, wanda ya ce Hukumar EFCC ta gayyace shi kan zargin sha’anin kudi bayan wa’adinsa ya kare a matsayin Mataimakin Gwamnan Jihar Bayelsa.

A baya-bayan nan mawakin ya ce tsohon shugaban Najeriya ya taba zuwa EFCC a matsayin wanda aka yi wa tambayoyi ko gudanar da bincike a kan shi, sai dai wata sanarwa da tsohon shugaban ya fitar ta musanta hakan.

A ranar Juma’a ne Wealth Dickson Ominabo wanda jami’in yada labarai ne a ofishin tsohon Shugaban Kasar ya fitar da sanarwar da ta karyata wannan ikirarin.

Ominabo ya ce ya yi amfani da wasu bayanai da wasu suka rika yada wa a baya kan shugaban domin su bata masa sunan, har suka rika cewa sai da ya je EFCC domin amsa tambayoyi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *