Dan majalisa ya rasu kwana 3 da rantsar da shi

Mamba mai wakiltar mazabar Chikun a majalisar dokokin jihar Kaduna a karkashin inuwar jam’iyyar PDP Madami Garba Madami ya koma ga mahalicci.

Mun ta tattaro cewa Madami ya rasu ne a asibitin da yake jinya ranar Asabar, kwanaki uku da rantsar da shi a matsayin dan majalisa.

An rantsar da ’yan majalisar jiha ta 10 ne a ranar 13 ga watan Yunin 2023.

Haka kuma marigayi dan majalisar bai iya halartar majalisar ba sakamakon wata rashin lafiya da ba a bayyana ba.

An ruwaito cewa wani mai sarautar gargajiya daga mazabarsa (Chikun), Ibrahim Sale, Ardo Ardodin, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *