Tinubu ya naɗa masu ba shi shawara kan harkoki daban-daban

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya naɗa masu ba shi shawara kan harkoki daban- daban ciki har da Mallam Nuhu Ribaɗu a matsayin mai ba shi shawara kan harkokin tsaro na musamman.

A Wata sanarwa da Abiodun Oladunjoye, daraktan yaɗa labarai a fadar shugaban kasar ya fitar ta ce Shugaba Tinubu ya amince da naɗe-naɗen da suka haɗar da Dele Alake a matsayin mai bashi shawara kan harkar ayyuka na musamman.

Akwai kuma Mallam Ya’u Darazo a matsayin mai ba da shawara na musamman kan harkokin siyasa da hulɗa tsakanin gwamnatoci.

Haka zalika, Tinubu ya amince da naɗa Mista Wale Edun a matsayin mai ba da shawara na musamman kan manufofin kuɗi.

Akwai kuma mai ba da shawara ta musamman kan harkokin makamashi, inda Tinubu ya naɗa Misis Olu Verheijen.

An kuma naɗa Dr. Salma Ibrahim Anas a muƙamin mai ba da shawara ta musamman a fannin kula da lafiya.

Sai kuma Mista John Ugochukwu wanda aka naɗa mai ba da shawara na musamman kan harkokin masana’antu, kasuwanci da zuba jari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *