Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya karbi bakuncin mai kudin Afrika, Alhaji Aliko Dangote a fadar shugaban kasa da ke Abuja a ranar Juma’a, 16 ga watan Yuni.
Dangote ya shiga jerin manyan masu ruwa da tsakin da suka zaiyarci Shugaban kasa Tinubu tun bayan da ya hau karagar mulki a ranar Litinin, 29 ga watan Mayu.
Sai dai kuma, ba a tabbatar da abun da ganawar tasu ta kunsa ba amma akwai alamu da ke nuna kawai ziyarar ban girma ce ko kuma dai jiga-jigan kasar biyu sun tattauna ne game da yiwuwar hada kai don bunkasa tattalin arzikin Najeriya.