Tinubu ya kaddamar daMajalisar tattalin arziki ta kasa (NEC)

Shugaban Kasa Bola Tinubu ya kaddamar da Majalisar tattalin arziki ta kasa (NEC) karkashin jagorancin mataimakin Shugaban kasa Kashim Shatima, a wani bangare na kokarin gwamnatinsa na bunkasa tattalin arzikin Najeriya.

Shugaba Tinubu ya nada mataimakinsa Kashim Shatima a matsayin shugaban Majalisar da kuma wasu muhimman mambobin Majalisar da suka hada da gwamnonin jihohi 36, gwamnan babban
bankin kasa, Ministan kudi, da sauran shugabannin hukumomin gwamnati da abin ya shafa.

Babban makasudin Majalisar ta (NEC) shi ne aiwatarwa da bayar da shawarwari masu ma’ana kan tsarin gwamnati na ci gaban tattalin arziki.

Shugaba Tinubu ya bayyana kudurinsa na gudanar da mulki ba tare da son rai ba, tare da tabbatar da cewa, gwamnatin tana gudanar da ayyukanta kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada da kuma bin doka da oda.

A yayin jawabin da ya yi wa Majalisar ta tattalin arzikin kasa, Shugaba Tinubu ya bayyana irin sadaukarwar da gwamnatin ke yi na inganta rayuwar ‘yan Nijeriya.

Ya kuma jaddada muhimmancin gudanar da mulki da ke bin kundin tsarin mulki da bin doka da oda, tare da kare al’ummar kasar daga ta’addanci da ayyukan laifuka daban- daban.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *