Maitamakin shugaban Kasa Kashim Shettima ya nemi al’ummar Musulmi Najeriya dasu yafe masa akan kalaman da yayi nacewa Komai lalacewar kirista Dan Kudu yafi nagartaccen masulmi daga Arewa ya shugabanci majalisar dattawa ta Kasa.
A cewarsa ba a fahimci maganar a sigarta ba, kuma ba shi da wata manufa na ɓata sunan addininsa.
Sanata Kashim a tattaunawarsa da BBC Hausa ya ce ya yi waɗannnan maganganu ne saboda maslahar Najeriya, ganin cewa suna da wasu bayanai na sirri da bai dace ya fito yana faɗi ba.

Sannan yace yadda lamura ke tafiya a Najeriya a wannan lokaci, dole shugabanni su fito su ja hankali domin wanzuwar kasar baki-ɗaya.
Kalaman Shettima a cikin makon da ya gabata ya haifar da zazzafar muhawara musamman a shafukan sada zumunta inda aka rinƙa sukar mataimakin shugaban kasa.
Sai dai Kashim Shettima ya ce shi Musulmi ne na haƙiƙa domin zuri’arsu sun shafe tsawon dubban shekaru kan tafarkin addinin Islama.
Sannan duk wanda bai jidadin kalamansa ba, ya yi hakuri a yafe masa, ba shi da niyyar cutar da addini.
Kashim Shettima ya tunasar da cewa shi ɗan malamai ne kuma jikan malamai, don haka ba shi da niyyar muzantawa wani ɓangare na addinin kasar Nan