Kotu ta bada umarnin a mayar da motoci da sauran kayayyaki da aka kwashe daga gidan Matawalle

Wata babbar kotun tarayya da ke zaman ta a Gusau ta umarci rundunar ‘yan sandan Najeriya da wasu hukumomi hudu da ke da hannu wajen kwashe motoci da sauran kayayyaki daga gidajen tsohon Gwamnan Zamfara Bello Matawalle da su mayar da su cikin sa’o’i 48.

A ranar 9 ga watan Yuni ne ‘yan sanda tare da jami’an DSS da NSCDC suka kai samame a gidajen tsohon gwamnan a Gusau da Maradun inda suka yi awon-gaba da motoci da wasu kayan gwamnan da na iyalansa bisa umarnin wata karamar kotu.

Daga baya a wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar ta ce ta kwato motoci 40 a lokacin samamen amma ta yi shiru kan sauran kayan da tsohon gwamnan ya yi zargin an kwashe.

Alƙalin kotun mai shari’a A.B Aliyu, ya umurci waɗanda ake ƙara da su mayar da dukkanin motoci da sauran kayan da suka kwashe, tare da bayani a rubuce kan dukkanin kayan, sannan su miƙa su ga kotu.

Kotun ta kuma bayar da umarnin dakatar da wadanda ake ƙarar da suka hada da rundunar ‘yan sandan Najeriya, da sufeto janar na ‘yan sanda, da kwamishinan ‘yan sandan jihar Zamfara da hukumar DSS da kuma NSCDC daga ɗaukar wani mataki dangane da lamarin tare da dakatar da duk wani mataki da za a dauka har sai an saurari karar da ke gaban kotun a ranan 28 ga watan Yuni.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *