An umarci DSS su gaggauta bai Emefiele damar ganawa da lauyoyinsa da iyalansa

An umarci babban daraktan hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da hukumar DSS din kanta da
su gaggauta bai wa gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) da aka dakatar, Godwin Emefiele
damar ganawa da lauyoyinsa da iyalansa ba tare da ɓata lokaci ba, kamar yadda tsarin mulki ya
tanadar.

Umarnin ya fito ne daga mai shari’a Hamza Muazu na babbar kotun birnin tarayya da ke zamanta a Maitama Abuja a ranar Juma’a.

Lauyan Emefiele JB Daudu ya sanar da kotun cewa ya rubuta wa hukumar DSS wasiku, musamman a ranar 14 ga watan Yuni domin neman ƙarin umarni daga wurinsa, amma hukumar DSS ta ƙi amsa buƙatar.

A ɗaya ɓangaren kuma lauyan waɗanda ake ƙara na biyu da na uku, I. Awo, ya shaida wa kotun cewa hukumar DSS ba ta da hurumin ƙin amincewa da wannan buƙata, kuma yin hakan ba daidai ba ne.

Sai dai ya bayyana tabbacin hukumar tsaron za ta bi umarnin kotu tare da bai wa lauyoyin da aka
lissafa da kuma iyalan Emefiele damar ganin sa.

Hukumar DSS ta kama Emefiele a ranar Asabar, sa’o’i kaɗan bayan shugaba Bola Tinubu dakatar
da shi daga muƙaminsa a yammacin Juma’a.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *