Tinubu ya ba da umarnin kai kayan agaji ga mutanen da suka kuɓuta da kuma dangi da iyalanwaɗanda suka mutu a hatsarin jirgin ruwan Kwara.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ba da umarnin kai kayan agaji da taimakon da ya wajaba nan take ga mutanen da suka kuɓuta da kuma dangi da iyalan waɗanda suka mutu a hatsarin jirgin ruwan Kwara.

A Wata sanarwa daga daraktan yaɗa labarai ga shugaban Najeriyar, Abiodun Oladunjoye ta ambato Bola Ahmed Tinubu na cewa ya yi takaicin wannan hatsarin jirgin ruwa da ya kashe mutum 150 a jihar Kwara.

Ya kuma umarci gwamnatin jihar Kwara da sauran hukumomin gwamnatin tarayya da lamarin ya shafa su yi aiki tare don gano sanadi na kusa da na nesa da suka janyo aukuwar hatsarin jirgin ruwan.

Mutanen da hatsarin ya ritsa da su ‘yan biki ne da ke komawa gida daga ƙauyen Egbu a cikin ƙaramar hukumar Patigi.

Cikin fasinjojin jirgin ruwan har da wani uba da ke tare da ‘ya’yansa guda huɗu – kuma har zuwa yanzu ba a san halin da suke ciki ba.

Shugaban ya kuma yi alƙawarin cewa gwamnatinsa za ta yi nazari kan matsalolin sufurin ruwa a ƙasar nan don tabbatar da ganin ana aiki sau da ƙafa da matakan kare rayuka da ƙa’idojin aiki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *