Tinubu ya ƙaddamar da majalisar tattalin arzikinkasa

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ƙaddamar da majalisar tattalin arzikin kasa.

An kaddamar da majalisar ne ƙarƙashin jagorancin mataimakin shugaban ƙasar Sanata Kashim Shettima a zauren majalisar da safiyar wannan rana A wani saƙo da Dada Olusegun, mataimaki na musamman ga shugaban ƙasar ya wallafa a shafinsa na twitter ya ce an ƙaddamar da majalisar ne a zaurenta da ke fadar shugaban ƙasa a Abuja.

Ƙwarya-ƙwaryar bikin ya samu halartar shugaban ma’aikata na fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila, da Sakataren gwamnatin tarayya Sanata George Akume da gwamnonin jihohin ƙasar 36.

Da yake jawabi a lokacin ƙaddamar da majalisar, shugaban ƙasar ya buƙaci gwamnonin dasu haɗa kai, wajen bunƙasa ƙananan hukumomi da ababen more rayuwa, duba da manyan ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *