Majalisar dattawa ta dage zaman majalisar har zuwa ranar 4ga watan Yuli.

Majalisar dattawa, a ranar Laraba, ta dage zaman majalisar har zuwa ranar 4 ga watan Yuli.

Hakan ya biyo bayan amincewa da kudirin da mataimakin shugaban majalisar dattawa Sanata Barau Jibril ya gabatar a zauren majalisar a ranar Laraba.

Tunda farko dai Majalisar Dattawan ta amince da kudirin da ke sanar da shugaban kasa Bola Tinubu cewa an yi taron majalisar dattijai ta 10 da yawan kuri’u kuma an zabi shugabannin majalisar.

Haka kuma ta amince da kudirin rubuta wasikun taya murna ga kakakin majalisar wakilai da mataimakinsa kan zaben da suka yi.

Har ila yau, zauren majalisar ya amince da bukatar rubutawa hukumomin majalisar dokokin kasa da kasa, inda aka sanar da su cewa, an yi taron majalisar dattijai ta 10, kuma majalisar a shirye take ta karbi dukkanin wasu lamurra.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *