Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa, ta na shirin fara aiwatar da lamunin dalibai a watan Satumba zuwa Oktoban 2023.
Babban sakataren ma’aikatar ilimi ta tarayya, Andrew David Adejo ne ya bayyana hakan a Abuja yayin da yake zantawa da manema labarai kan kudirin dokar da shugaban kasa Bola Tinubu ya sanya wa hannu a kwanakin baya.
Kudirin lamuni ga dalibai wanda shugaban majalisar wakilai ta 9, Femi Gbajabiamila ya jagoranta, ya tanadi lamuni marar ruwa ga daliban Nijeriya marasa galihu.
Dokar dai a takaice, ita ce samar da hanyoyin samun ilimi mai sauki ga ‘yan Najeriya marasa galihu ta hanyar bayar da lamuni mara ruwa daga asusun lamuni na ilimi na Nijeriya kamar yanda babban sakataren ya bayyana.