EFCC ta gayyaci Hadi Sirika don amsa tambayoyi.

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta gayyaci tsohon ministan sufurin jiragen sama karkashin tsohuwar gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, Hadi Sirika, don amsa tambayoyi.

Hukumar ta yi wa jami’an kamfanin jirgin saman Najeriya tambayoyi kan aikin kaddamar da jirgin da tsohon ministan ya yi a kuraren lokaci a Abuja.

Ana sa ran tsohon ministan zai gurfana a gaban hukumar yaki da rashawar cikin makon nan don amsa tambayoyi dangane da kaddamar da jirgin saman Najeriyan da aka kawata da kalar Habasha.

Wilson Uwujaren, kakakin hukumar EFCC, ya tabbatar da cewa ana gudanar da bincike amma bai bayar da cikakken bayani ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *