An nada Abdulkarim Chukkol a matsayin mukaddashin shugaban EFCC

An nada Abdulkarim Chukkol a matsayin mukaddashin shugaban hukumar yaki da cin hanci da Rashawa ta EFCC, biyo bayan dakatar da Abdurashid Bawa da shugaban Najeriya Bola Tinubu yayi a ranar Laraba.

A wata Sanarwa mai dauke da sa hannun daraktan yada labaran ofishin sakataren gwamnatin tarayya Willie Bassey, da aka fitar ta umurci Bawa da ya mikawa daraktan ayyuka na hukumar ta EFCC.

A shekarar 2003 Chukkol ya fara aiki da hukummar EFCC, inda ya kai ga zama babban jami’in bincike da kuma daraktan ayyuka.

Jami’in dan sandan ya taba shugabantar ofishin shiyya na EFCC dake garin Fatakwal, kafin a mayar da shi hedikwatar hukumar da ke Abuja.

Abdulkarim Chukkol, wanda babban jami’in bincike ne a hukumar, zai ci gaba da jan ragamar hukumar har zuwa lokacin da za a nada sabon shugaba.

Chukkol ya yi digirinsa na farko a fannin Kimiyya a Jami’ar Maiduguri a 2000, sannan ya yi karatun Difloma a fannin Shari’a a Jami’ar Virginia da ke kasar Amurka a 2011.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *