Sabon shugaban majalisar dattawa kuma tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom, Godswill Akpabio, ya sha
alwashin cewa majalisar dattawa ta 10 za ta zarce abin da ‘yan Najeriya ke zato wajen gina kasa.
Akpabio ya yi wannan alkawarin ne a lokacin da yake gabatar da jawabinsa na farko bayan rantsar da shi a
Abuja ranar Talata.
Idan za a iya tunawa, Akpabio, wanda shi ne dan takarar jam’iyyar APC mai mulkin kasa an rantsar da shi a
matsayin shugaban majalisar dattawa ne bayan ya samu kuri’u 63, inda ya doke abokin takararsa,
Abdulaziz Yari, wanda ya samu kuri’u 46.