Jim kaɗan bayan gwamnatin Kano ta rusa shataletalengidan gwamnatin jihar, masu ɗibar ‘ganima’ sun dira wurin

Jim kaɗan bayan gwamnatin Kano ta rusa shataletalen gidan gwamnatin jihar, masu ɗibar ‘ganima’ sun dira a wurin domin kwasar ƙarafan rodi da sauran abubuwan amfani.

Rahotonnin sun ce an wayi gari ne kawai da ganin motocin rusau a kan ginin shataletalen da ke gaban gidan gwamnatin jihar.

Mutane musamman a shafukan sada zumunta na ta bayyana mabambantan ra’ayoyi game da rusa ginin,
wanda aka gina domin bikin cikar jihar shekara 50 da kafuwa.

Kawo dai yanzu babu wani bayani daga gwamantin jihar Kano game da dalilin rusa ƙasaitaccen ginin.

A baya-bayan nan dai ana sukar sabuwar gwamnatin saboda rusa wasu wuraren da gwamnatin da ta gabata ƙarƙashin jagorancin Abdullahi Umar Ganduje ta gina, inda ta yi zargin cewa an yi gine-ginen ne a filayen da aka mallakesu ba bisa ƙa’ida ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *