‘Ba za mu zama ‘yan amshin shataba yayin wa’adin mulkin mu’ – Tajudeen Abbas

Sabon Kakakin Majalisar Wakilan kasa Tajudeen Abbas, ya ce, ba za su zama ‘yan amshin shata
ba yayin wa’adin mulkinsu.

Ya bayyana hakan ne ga manema labarai a Abuja bayan wata ganawa da ya yi da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a ofishinsa.

An zabi Abbas a matsayin shugaban majalisar ta wakilai bayan da ya samu gagarumar nasara a ranar Talata.

A lokuta da dama, akan zargi ‘yan majalisar dokoki da zama ‘yan amshin shatar bangaren zartarwa, zargin da sukan musanta.

A cewar Abbas, za su dukufa wajen samar da tsare-tsare da za su ciyar da kasa gaba tare da hadin kan bangaren zartarwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *