Barau I. Jibrin, ya zama mataimakin shugaban majalisar dattawa

Zababben Sanatan Kano ta Arewa, Barau I. Jibrin, ya zama mataimakin shugaban majalisar dattawa ta 10 a safiyar yau Talata.

Nasarar Barau ta biyo bayan zaben Godswill Akpabio a matsayin shugaban majalisar dattawa.

Akpabio ya doke zababben Sanatan Zamfara ta Yamma, Abdul’aziz Yari, a zaben shugaban majalisar dattawa mai cike da rudani.

Zababben Sanatan Ebonyi ta Kudu, Dave Umahi ne ya tsayar da Barau, sai kuma zababben Sanata mai wakiltar Kwara ta tsakiya, Salihu Mustapha.

Bayan amincewa da nadin nasa ba tare da hamayya ba, magatakardan majalisar (CNA), Magaji Tambuwal, ya kara rufe zaben da misalin karfe 10 na safe.

Don haka sai aka nada Barau a matsayin mataimakin majalisar dattawan sannan kuma aka rantsar da shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *