‘Yan kasuwar magani A Kano Sun soma gudanar da zanga-zanga

Mambobin Ƙungiyar masu siyar da magani a kasuwar Bata, dake jihar Kano, sun gudanar da zanga-zangar lumana.

Zanga-zangar ta su na zuwa ne bayan da gwamnatin data gabata, ta bayyana kammala shirin ta na mayar da su zuwa kasuwar Dangoro, Maimaikon barin su domin ci gaba da zama a kasuwar.

Wannan mataki da yan kungiyar suka dauka, yana da alaqa da burin su na nuna rashin goyon bayan atashe su daga kasuwar.

Shugaban ƙungiyar ƴan kasuwar maganin na riƙon ƙwarya, Musbahu Yahaya Khalid, shi ne ya jagoranci zanga-zangar da safiyar ranar Litinin din nan.

Musbahu yayin zantarwarsa da Wakilinmu, ya bayyana cewa suna kira ga gwamnatin jihar Kano, ta fara duba ƙananan ƴan kasuwar da basu da damar kama shagunan a kasuwar Ɗangoro.

Wasu daga cikin ƴan kasuwar sun koka sun bayyana cewa ƙarfin su bai kai su kama shago a Dangoro ba, domin baza su iya kama shagon da ya kai naira miliyan ɗaya ba sakamakon basu da ƙarfin kama wa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *