Tinubu ya jinjinawa marigayi MKO Abiola

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya jinjinawa Marigayi MKO Abiola wanda ake kyautata zaton ya na kan hanyar lashe zaben shugaban kasa a 1993.

Tinubu ya na bayyana Mashood Kashimawo Abiola wanda ya mutu a gidan yari a matsayin ayar damukaradiyya.

Da yake magana, Shugaban kasan ya yarda mutanen Najeriya su na shan wahala a sakamakon tashin da
farashin man fetur ya yi saboda janye tallafi.

Bola Tinubu yake cewa gwamnatinsa za tayi wa al’umma sakayya ta hanyar manyan ayyukan more rayuwa a bangarorin sufuri da ilmin zamani.

Shugaban ya ce gwamnatin tarayya za ta maida hankali wajen samar da isasshen wutar lantarki, kiwon lafiya da sauran abubuwa na jin dadin rayuwa.

Tinubu yake cewa ya fahimci wahalar da ake sha, amma ya ce ba za a dawwama a wannan hali ba, ya kara da cewa janye tallafin fetur din ya zama dole.

Shugaba Tinubu ya jinjinawa Maraigayi MKO Abiola wanda ya kira shahidi a siyasa da ya sadaukar da
rayuwarsa domin ganin wanzurwar damukaradiyya.

Shugaban ya kuma yabi mutane irinsu Kudirat Abiola, da Alfred Rewane da Manjo Janar Shehu Yar’Adua wanda ya ce sun mutu a kan tafarkin tabbatar da dimokradiyyar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *