Ma’aikatar noma da raya karkara ta tarayya ta sanar da ‘yan Najeriya game da bullar cutar Anthrax

Ma’aikatar noma da raya karkara ta tarayya ta sanar da ‘yan Najeriya game da bullar cutar Anthrax da ke kama dabbobi a wasu kasashe makwabta na yankin yammacin Afirka.

Bisa wannan dalili ne ma’aikatar ta shawarci ‘yan Najeriya da su daina cin fatu da aka fi sani da ganda, da
naman dabbobin daji sakamakon hadarin da suke tattare da shi har sai an shawo kan lamarin.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban sakataren ma’aikatar, Dr Ernest Afolabi Umakhihe a yau Litinin.

Sanarwar ta ce an fara samun bullar cutar ne a arewacin Ghana mai iyaka da Burkina Faso da Togo lamarin da ya jefa yankin cikin hadari.

Sanarwar ta kuma gargadi jama’a game da cudanya da dabbobin da ba a yi musu allurar riga kafin cutar Anthrax ba, domin ana iya kamuwa da ita cikin sauki ta hanyar shakar kwayar cutar Anthrax da ta hada da cin naman dabbobin da suka kamu da cutar, ko cin fatarsu ko madara da sauransu.

Alamun kamuwa da cutar anthrax sun hadar da mura da tari, da zazzabi, da ciwon jiki kuma idan ba a gano cutar ba kuma an magance su da wuri, suna haifar da ciwon huhu, da wahalar numfashi, da firgita har ma ta kai ga rasa rai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *