“Ku daina cin ganda”: FG Ta Shawarci ‘Yan Najeriya Sakamakon Barkewar Wata Cuta

Gwamnatin Tarayya ta shawarci ‘yan Najeriya da su daina cin fatun da aka fi sani da (Ganda), da naman daji sakamakon barkewar cutar Anthrax a wasu kasashe makwabta.

Ma’aikatar noma da raya karkara ta tarayya ta bayar da wannan gargadi a ranar Litinin a wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban sakataren ma’aikatar noma da raya karkara ta tarayya Dr Ernest Umakhihe.

Umakhihe ya ce ya zama wajibi a fadakar da ‘yan Najeriya game da bullar cutar da ke addabar Arewacin Ghana da ke iyaka da Burkina Faso da Togo.

A cewarsa, cutar ta Anthrax ta na canjawa ne daga dabbobin da suka kamu da cutar zuwa mutum, saboda a dabi’ance ana samun cakuduwa, kuma yawanci hakan aka samu dabbobi da ake rayuwa da su ta yau da kullum.

Ko da yake mutane na iya kamuwa da ƙwayar cuta ta Anthrax idan sun yi mu’amala da dabbobi dake dauke da cutar, ko Kuma amfani da Wani sassa na jikin dabbar.

Alamominta sun hada da alamun mura kamar tari, zazzabi, ciwon tsoka kuma idan ba’a gano cutar ba kuma an magance su da wuri, yana haifar da ciwon huhu, matsananci, wahalar numfashi, firgita da ko ma mutuwa dungurum.

Ya ce, “Ma’aikatar Noma da Raya Karkara ta Tarayya tana sanar da jama’a game da barkewar cutar Anthrax a wasu kasashe makwabta na yankin Afirka ta Yamma; musamman, Arewacin Ghana iyakar Burkina Faso da Togo.

Babban Sakataren Ma’aikatar ya kuma yi kira ga Jihohin Sokoto, Kebbi, Niger, Kwara, Oyo, Ogun da Legas da su kara kaimi wajen yin allurar rigakafin dabbobi, saboda kusancinsu da Burkina Faso, Togo da Ghana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *