“Ko sisi ba su kashe ba wajen dauko hayar jirgin kamfanin EthiopianAirlines na kasar Habasha” – Hadi Sirika

Tsohon Ministan Sufuri, Hadi Sirika, ya ce ko sisi ba su kashe ba wajen dauko hayar jirgin kamfanin Ethiopian Airlines na kasar Habasha, wanda aka yi amfani da shi wajen kaddamar da jirgin Nigerian Air.

A baya an rawaito yadda Gwamnatin Tarayya ta ce ta dauko hayar jirgin samfurin Boeing 737-800, mallakin kasar ta Habasha, ana dab da tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya mika mulki.

Daga bisani dai Shugaban kamfanin na Nigeria Air da kansa ya amsa cewa hayar jirgin suka dauko domin
kaddamarwar, inda mutane suka yi ta sukar yadda aka kashe kudade wajen dauko hayar.

To sai dai yayin wata tattaunawa da gidan talabijin na Arise ranar Lahadi, tsohon Ministan ya karyata zargin da aka yi cewa sun kashe kudin wajen dauko hayar.

Ya kuma ce tun shekara ta 2016 da aka fara shirye- shiryen kaddamar da jirgin, Naira biliyan biyar kawai aka ware wa shirin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *