NNPCL ya musanta ikirarin cewa an dakatar da shugaban kamfanin

Kamfanin Kula da Albarkatun Man Fetur na Najeriya (NNPCL) ya musanta ikirarin cewa Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da shugaban kamfanin, Mele Kyari.

Dangane da dakatarwar da aka yi wa Gwamnan Babban Bankin Najeriya Godwin Emefiele a ranar Juma’a, an yi ta cece-kuce a shafukan sada zumunta na cewa an sauke Kyari daga mukaminsa Shima.

Sai dai a kamfanin ya musanta labarin a daren jiya Asabar ta hannun Garba Deen Muhammad, babban jami’in sadarwa na kamfanin NNPC, inda ya ce ikirarin ba gaskiya ba ne.

Ya nemi Yan Najeriya suyi watsi da labarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *