Matawalle ya koka da cewa sata aka je yi gidansa bayan gwamnatin jihar ta ƙwato wasu motoci daga gidan

Tsohon gwamnan Jihar Zamfara Bello Muhammad Matawalle, ya koka da cewa sata aka je yi gidansa bayan gwamnatin jihar ta ce ta ƙwato wasu motoci daga gidan nasa da gwamnan ya ƙi mayarwa gidan gwamnati.

A ranar Juma’a ne gwamnatin Zamfara ƙarƙashin jagorancin Dauda Lawal ta ce jami’an tsaro sun shiga
gidajen Matawalle biyu, a Gusau da kuma Maradun, inda suka ƙwato motoci har 40.

Sai dai Matawalle ya ce “sakarci ne” da “talauci” ya sa aka shiga gidan nasa, ya na mai cewa an sace kayayyaki ciki har da hijabin matansa.

Tsohon gwamnan na zamfara Ya ƙara da cewa wasu daga cikin motocin da aka kwashe ya saye su ne daga Amurka tun kafin ya zama gwamna saboda da ma sana’arsa ce sayar da motoci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *