Majalisa ta 9 ta karɓi ƙorafi 705 daga ɗiɗaikun ‘yan ƙasar cikin shekara 4 – Ahmad Lawan

Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya mai barin gado,Ahmad Ibrahim Lawan, ya ce Majalisa ta Tara da ya jagoranta ta karɓi ƙorafi 705 daga ɗiɗaikun ‘yan ƙasar cikin shekara huɗu.

Da yake jawabin bankwana a ranar Asabar a zauren Majalisar, Ahmad Lawan ya ce sun samu ƙorafi 146 a
shekarar farko, 239 a shekara ta biyu, 232 a shekara ta uku, da kuma 88 a ta uku.

Kazalika, ‘yan Majalisa ta Tara sun gabatar da ƙudiri 361 (motion) sannan kuma suka ɗauki matsaya (resolution) 488 a kan batutuwa daban-daban da suka ja hankalin gwamnati
a kansu, a cewarsa.

A ranar Talata mai zuwa ake sa ran za a rantsar da Majalisa ta 10, yayin da ake ci gaba da tafka siyasa game da wanda zai maye gurbin Ahmad Lawan a matsayin shugaba.

Jam’iyyar APC mai mulki dai na son ‘yan majalisar su zaɓi Godswill Akpabio daga Jihar Akwa Ibom a kudancin Najeriya, a matsayin shugaba, da kuma Barau Jibrin daga Kano a arewacin ƙasar a matsayin mataimakinsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *