Dije Aboki ta yabawa kokarin kwamishinan ‘yan sandan Kano na kawo karshen kwacen wayar salula a jihar

Babbar Maishariah ta jihar Kano Dije Aboki ta yabawa kokarin kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano na kawo karshen kwacen wayar salula a jihar nan.

Mai shariah ta jahar kano Dije Aboki ta fadi hakanne ayayin maraba ga kwamishinan ‘Yan sandan jahar kano cp muhd hussaini gumel ayayin wata ziyarar aiki da ya kai mata ofishinta.

Mai shariah Dije Aboki ta ce su a bangaren shari’ah sun daura damarar ganin kotuna na hukunta wadanda aka samu da laifi sai dai ta koka da cewa rashin bayyanar ‘yan sanda don ba da sheda a kotu na haifar da jan kafa wajen zartar da hukunci ga wadanda ake tuhuma.

Dije Aboki ta bukaci ‘yan sanda da su rika ziyartar wuraren da aka tafka lefi a maimakon dogara da bayanan wanda ake tuhuma da tafka wani lefi kuma tace ake rubuta bayanan wadanda ake zargi a harshen da su ke iya fahinta.

Tunda farko kwamishinan ‘yan sandan jahar kano CP Muhammad hussaini gumel ya ce zun kai ziyarar ne don taya murna ga nadin da akaiwa Babbar mai shari’ah ta jIhar Kano Justice Dije Aboki a matsayin Mukaddashiya.

A donhaka ya buakaci a sami karin fahinta atsakanin rundunar ‘yansanda da kuma fannin shariahdon kawo karshen kwacen wayar salula.

Cp muhd hussaini gumel ya ce sun cafke mutane 400 bisa zarginsu da kwacen wayoyin salula a jIhar Kano kuma tuni su ka gurfanar da su a gaban kotu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *