Tinubu Ya Dakatar Da Emefiele A Matsayin Gwamnan CBN

Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da Godwin Emefiele a matsayin gwamnan babban bankin Nijeriya (CBN).

“Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da gwamnan babban bankin kasa, Mista Godwin Emefiele, daga aiki ba tare da bata lokaci ba,” in ji daraktan yada labaran gwamnatin tarayya, Willie Bassey a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a.

“Wannan ya biyo bayan binciken da ake yi a ofishinsa da kuma sauye-sauyen da ake shirin yi a bangaren hada-hadar kudi na tattalin arzikin kasar nan.

“An umarci Mista Emefiele da ya gaggauta mika al’amuran ofishinsa ga Mataimakin Gwamnan na bangaren Ayyuka wanda zai yi aiki a matsayin Gwamnan Babban Bankin kasar nan har sai an kammala bincike da kuma gyara.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *