Tinubu ya bayyana alhininsa kan rasuwar Sheikh Nasir Muhammad Nasir

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana alhininsa kan rasuwar babban limamin Kano, Sheikh Nasir Muhammad Nasir Shugaban a cikin wata sanarwa da Daraktan yada labarai Abiodun Oladunjoye ya fitar.

Ya bayyana rasuwar malamin a matsayin rashi ga kasar nan duba da irin gudunmawar da ya bayar wajen yada ilimi da kuma gyara.

Sanarwar tace za’a dade ana tunawa da Sheikh Nasir wanda ya sadaukar da kusan dukkanin rayuwarsa wajen neman ilimi da shayar da ilimi.

Shugaban kasar ya jajantawa iyalansa,da mabiyansa, da sarakunan Kano dana Bichi da kuma gwamnatin jihar Kano bisa wannan babban rashi.

Inda yayi addu’ar Allah yaji kansa ya kuma gafarta masa ARMY Wani soja ya gamu da ajalinsa a yayinda jirgin kasa ya kade shi a yankin PWD da ke Ikeja a Jihar Legas.

Jirgin kasan ya kashe sojan ne adaidai wurin da wani jirgin kasa ya kashe mutum shida, ya kuma jikkata wasu 80 a cikin motar jigilar ma’aikatan Gwamnatin Jihar Legsa.

Shaidu gani da ido sun ce, sojan mai mukamin Sajan, ya gamu da ajalinsa ne bayan ya yi kokarin tsallake titin jirgin a kan babur dinsa

Wata majiya ta ce an sanar da Birged na 9 na Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya, inda sojan yake aiki, kuma sun dauke gawar mamacin zuwa Asibitin Sojoji da ke Yaba a jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *