Hukumar shirya jarabawar shiga Jami’o’in kasarnan ta JAMB ta fitar da tsarin da za’abi wajen karbar daliban da suka dawo daga kasasshen da yaki ya tilasta musu dawowa Jami’o’in Najeriya.
Hukumar ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da shugaban hukumar,kuma jami’in hulda da jama’a da tsare-tsare Dakta Fabian Banjamin ya rabawa manema labarai a Abuja.
Banjamin ya ce tsarin ya biyo bayan babban taron da aka yi tsakanin ma’aikatar ilimi ta tarayya, da ma’aikatar lafiya ta tarayya, da hukumar JAMB, da Hukumar kula da yan Nijeriya mazauna kasashen waje, da kuma hukumar kula da Jami’o’i ta Kasa da sauran masu ruwa da tsaki.
Ya ce taron nada nadaba da shigar da daliban Najeriya da suka dawo daga kasashen da rikici ya dabaibaye cikin tsarin ilimin manyan makarantun kasar.
Ya kara da cewar ya zama wajibi a tattauna da shugabannin Jami’o’i biyo bayan irin abubuwan da kowace jami’a taje dasu da kuma bambancin martanin da aka samu daga wajen sukar lamarin.
Ya kuma bayyana cewar kowace majalisar zartaswar jami’a tana da ‘yancin yanke shawara kan canza bukatar ba sai ta jira hukumar JAMB ta fara gudanar da haka ba.