“Da na hadu da Kwankwaso a fadar shugaban kasa da na gaura masa mari” – Ganduje

Tsohon Gwamnan Jihar Kano da ke Najeriya Abdullahi Umar Ganduje ya ce, da ya sharara wa tsohon mai gidansa, Rabiu Musa Kwankwaso mari muddin ya yi ido biyu da shi a fadar shugaban kasa da ke birnin Abuja.

Wannan na zuwa ne a yayin da Kwankwaso ya gana da shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu a fadarsa a ranar Juma’ar nan.

A yayin zantawa da manema labarai a fadar ta shugaban kasa, Ganduje ya bayyana rashin jin dadinsa da matakan da sabuwar gwamnatin jihar Kano ke dauka na rushe-rushen gideje.

Ganduje ya ci gaba da cewa, yana da masaniyar cewa, Kwankwaso na cikin fadar shugaban kasar amma ba su hadu ba. Sai dai akwai yiwuwar na sharara masa mari idan muka gamu a cewarsa.

Muryar Ganduje kan marin Kwankwaso cikin harshen Turanci

Na san yana cikin ginin, amma ba mu hadu ba, watakila da mun hadu da na zabga masa mari- inji Ganduje

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *