Shugaban Kasa Bola Tinubu, ya yi kira ga Gwamnoni da su hada kai da Gwamnatin Tarayya wajen yaki da talauci a Najeriya.
Shugaban, wanda ya yi wannan kiran lokacin da ya karbi Gwamnonin Najeriya a fadarsa da ke Abuja ranar Laraba ya ce yawan talaucin ba abin da za a lamunta ba ne.
Tinubu ya kuma yi kira ga ’yan siyasa da su manta da bambance-bambancensu su hada gwiwa wajen kakkabe talauci a Najeriya.
Shugaba Tinubu ya kuma ce shugabanci na gari ne zai tabbatar da ci gaban Dimokuradiyya a Najeriya.
Kazalika, ya kuma ba Gwamnonin tabbacin cewa kofarsa za ta zama a bude ga dukkan Gwamnonin.