Shugaban Kasa Bola Tinubu a ranar Alhamis din nan ya rattaba hannh a kan kudirin dokar shekarun ritayar ma’aikatan shari’a
Mun tattaro cewa Kudirin dokar wanda shi ne don tabbatar da daidato a shekarun ritaya da kuma hakkin fansho na jami’an shari’a.
Dokar wacce za ta shafi alkalai shari’a na manyan kotuna da kuma tsawaita shekarun ritaya daga shekara 65 zuwa 70.
Jaridar Solacebace ta rawaito cewa Kudirin ya bayyana jami’an sheri’a na manyan kotuna kamar haka: “ma’aikacin shari’a da aka nada shi zuwa kotun koli, kotun daukaka kara, babbar kotun tarayya, kotun da’ar ma’aikata ta Kasa“.
Sauran su ne alkalan “babbar kotun daukaka kara ta birnin tarayya Abuja, babbar kotun shari’a ta jiha, kotun daukaka kara ta jiha na iya yin ritaya idan ya/ta cika shekara 65 da haihuwa zai kammala aikin rike mukaminsa idan ya/ta kai shekara 70”