Rundunar sojin Najeriya ta ce ta damu da yadda ayyukan ‘yan ta’adda ke sake kunno kai a wasu yankuna, kuma ba za ta yarda a ci gaba da salwantar da rayukan jama’a tana kallo ba.
Wannan na zuwa ne lokacin da rundunar ta ke samun kwarin gwiwa daga wasu gwamnatoci a kokarin ta na samar da tsaro a Najeriya.
Bayanan da ke fitowa daga wasu sassa na Najeriya sun nuna cewa ‘yan bindiga na zafafa kai hare-hare ga jama’a kwanannan musamman a wasu yankunan arewa maso yammacin kasar.
Jihar Sakkwato na daga cikin wuraren da ‘yan bindigar suke kai hari ga jama’a, inda a kasa da mako daya an sami kai hare-hare da satar mutane a yankuna da suka hada da Kware, Illela, Gwadabawa, Sabon Birni, Wurno da Isa inda jama’a ke ta kokawa.
Damuwa da sake bullar matsalar ne musamman a karamar hukumar Tangaza ya sa rundunar sojin Najeriya ta ce ba za ta saka ido ana yi wa jama’a kisan gilla ba.
Shugaban yanki na 8 na rundunar sojin Najeriya mai hedikwata a Sakkwato Manjo Janar Godwin Mutkut ya ce tuni sun soma aikin dakile ayyukan ‘yan bindigan.