DAPPMAN zata samar da manyan motocin bas 100 don tallafa wa yunƙurin gwamnati na cire tallafin man fetur.

Ƙungiyar dillancin man fetur a Najeriya ta Depots and Petroleum Products Marketers Association of Nigeria (DAPPMAN) ta yi alƙawarin samar da manyan motocin bas 100 don tallafa wa yunƙurin gwamnati na cire tallafin man fetur.

Da take magana bayan ganawarsu da Shugaba Bola Tinubu ranar Laraba, shugabar ƙungiyar Dame Winifred Akpani ta ce suna goyon bayan matakin gwamnati na cire tallafin 100 bisa 100.

Akpani ta ce motocin ƙirar gida ne kuma masu amfani da iskar gas maimakon fetur.
Tun farko gamayyar ƙungiyoyin ƙwadago a Najeriya sun shirya tsunduma yajin aikin gama-gari amma daga baya suka janye bayan su gana da shugaban ƙasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *