Tinubu ya gana ƴan takarar da ke neman shugabancin majalisar wakilai ta 10

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gana da wasu daga cikin ƴan takarar da ke neman shugabancin majalisar wakilai ta 10 Shugaban ƙasar ya gana da biyar daga cikin ƴan takarar masu adawa da zaɓin da jam’iyyar APC ta yi kan shugabancin majalisar

Shugaban ƙasar ya kuma sanya labule da mataimakin kakakin majalisar wakilai, Idris Wase, wanda yana ɗaya daga cikin masu neman kujerar kakakin majalisa ta 10.

Zaman na su ya samu halartar shugabancin jam’iyyar (APC), ciki har da sakataren jam’iyyar na ƙasa Sanata Iyiola Omisore.

Kazalika Shugaba Tinubu ya kuma sanya labule da tsohon gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Ganduje da kuma shugaban hukumar yaƙi da cin hanci ta ƙasa (EFCC), Abdulrasheed Bawa.

Duk da dai cikakkun bayanai ba su gama fitowa ba dangane da zaman da shugaban ƙasar ya yi da ƴan takarar, zaman na su baya rasa nasaba da batun rikicin shugabancin majalisar.

Jam’iyyar APC da shugaba Tinubu sun zaɓi Abbas Tajudeen da Benjamin Kalu, a matsayin ƴan takararsu a kujerar kakakin majalisae wakilai ta 10.

Wannna zaɓin na su dai ya fusata sauran ƴan takarar da ke neman kujerar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *