Lai Muhammad ya samu sabon mukami

An nada tsohon ministan yada labarai da al’adu a zamanin gwamnatin Buhari Lai Muhammad a matsayin babban manajan na kamfanin Ballard Partners.

Mun tattaro cewa Kamfanin Ballard Partners wani kamfani ne da ke fafutukar hulda da gwamnati a fadin Duniya.

Wannan na zuwa ne kasa da makonni biyu da rusa majalisar ministocin tsohon shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

An tabbatar da sabon nacin Lai a cikin wata sanarwa da aka wallafa a shafin yanar gizon Twitter na kamfanin a ranar Talata.

An nakalto ” Ballard Partners daya daga cikin manyan kamfanonin hulda da gwamnati a Amurka ya bude ofishinsa na farko a Afirka a Abuja, babban birnin tarayyar Nijeriya “

Lai Muhammad tsohon ministan yada labarai da al’adu na Nigeria zai yi aiki a matsayin babban mai gudanarwa na ofishin Abuja da ofishin tauraron dan Adam na kamfanin Legas, cibiyar hada-hadar kudi ta kasa“.

 Jaridar Daily Post ta rawaito cewa, Shugaban kamfanin ya bayyana cewa an baiwa mista Lai mukamin saboda “yana daya daga cikin mutanen da ake girmamawa a Kasar”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *