Tinubu ya sha alwashin inganta mafi karancin albashin ma’aikata a Nigeria.

Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, ya ce zai inganta rayuwar ‘yan Nijeriya wanda shi ne babban manufar gwamnatinsa.

Shugaban wanda ya karbi bakuncin kungiyar gwamnonin APC, karkashin jagorancin shugaban kungiyar, Gwamna Hope Uzodinma, na Jihar Imo, a fadar gwamnati, ya ce gwamnatocin kasa da na kananan hukumomi za su yi aiki tare a kan mafi karancin albashin ma’aikata, wanda tuni ya fara aiki.

A wata sanarwa da daraktan yada labarai, Abiodun Oladunjoye ya fitar, shugaba Tinubu ya bukaci gwamnonin da su yi amfani da damar da aka basu na zabar su a cikin miliyoyin al’ummar jihohinsu domin kawo sauyi a rayuwar jama’a, inda ya kara da cewa zai yi aiki da su domin amfanar da ‘yan Nijeriya.

Shugaban wanda ya karbi bakuncin kungiyar gwamnonin APC, karkashin jagorancin shugaban kungiyar, Gwamna Hope Uzodinma, na Jihar Imo, a fadar gwamnati, ya ce gwamnatocin kasa da na kananan hukumomi za su yi aiki tare a kan mafi karancin albashin ma’aikata, wanda tuni ya fara aiki.

A wata sanarwa da daraktan yada labarai, Abiodun Oladunjoye ya fitar, shugaba Tinubu ya bukaci gwamnonin da su yi amfani da damar da aka basu na zabar su a cikin miliyoyin al’ummar
jihohinsu domin kawo sauyi a rayuwar jama’a, inda ya kara da cewa zai yi aiki da su domin amfanar da ‘yan Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *