Kungiyar kwadagon ta Kasa ta ce za ta shiga yajin aiki a makon gobe, bayan da gwamnatin Nigeria ta sanar da shirin janye tallafin man fetur.
Shugaban kungiyar ta NLC, Joe Ajaero, shine ya sanar da matakin, bayan wani taron tattaunawa da kungiyar ta gudanar a Abuja, babban birnin kasar.
Ajaero yace, NLC ta bawa Kamfanin main a kasar NNPC, wa’adin zuwa ranar Laraba mai zuwa, da ya janye karin kudin man fetur da aka yi a fadin kasar, ko kuma su dauki matakan da suka dace.
Ya kara da cewa, matsawar gwamnatin Najeriya ta gaza sassauta farashin man, to kuwa za su shiga yajin aiki na sai baba ta gani.
yayin jawabin da ya gabatar ranar litinin, a wurin taron bikin rantsuwar kama aiki, sabon shugaban Najeiyar, Bola Ahmed Tinubu, ya ce an kawo karshen tallafin man fetur da gwamnati ke
biya, tare da cewa babu batun tallafin a cikin kasafin kudin shekarar 2023 da aka amince da shi.
Maimakon biyan tallafin man na fetur, Tinubu y ace gwamnatinsa za ta yi amfani da kudaden wajen samar da ababen more rayuwa ga ‘yan Najeriya, da kuma samar da hanyoyin inganta tattalin
arzikin kasar.