Gwamnan Kano ya dada jadda umarninsa na rushe dukkanin gine gine da akayi ba bisa ka’ida ba

Gwamnan Kano Abba kabir Yusuf ya dada jadda umarninsa na rushe dukkanin wasu gine gine da akai ba bisa ka’ida ba ‘a Jihar nan.

Da yake jawabi yayin da yakai ziyarar gani da Ido sansanin Alhazai na jihar Kano Abba kabir Yusuf yace badan kurewar lokaci ba, da Babu makawa sai ya mayar da sansanin hayyacinsa.

Amma Duk da haka ya umarci masu gine gine a sansanin Alhazan da su dakata kafin su Hadu da fushin Hukuma kuma yasha alwashin yin duk Mai yiyuwa dan ganin maniyyata da zasu tashi ta Jihar Kano sun Sami dukkanin kulawa.

Gwamna Abba kabir yusuf ya yabawa Saban shugaban hukumar jin dadin Alhazai ta jahar Kano saboda kawo cikakken rahotan duk wata matsala da ta shafi Alhazan akasa da awa goma 12 da nada shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *