Babangida ya bukaci Tinubu da ya magance kalubalentattalin arzikin a Najeriya

Tsohon Shugaban kasa, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB), ya bukaci zababben Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu da ya yi amfani da kwarewarsa wajen magance kalubalen tattalin arzikin da Nijeriya ke fuskanta cikin gaggawa.

Babangida ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da gidan talabijin na Arise TB, inda ya kuma taya Shugaban kasa, Tinubu da mataimakin Shugaban kasa, Kashim Shettima murna rantsar
da su da aka yi.

Haka kuma IBB ya bayyana Tinubu a matsayin hazikin dan siyasa, yayin da ya bukace shi da ya sake fasalin rundunar sojojin Nijeriya da kuma zaburar da manyan masu karfin tattalin arzikin kasar nan wajen zuba jari.

Babangida ya kuma bukaci ‘yan Nijeriya su yi hakuri da sabuwar gwamnatin Tinubu.

Ya jaddada cewa, Tinubu na bukatar samun damar hada kan Najeriya, yana mai bayyana ra’ayin cewa akwai mutane masu basira da za su iya taimaka masa wajen gyara kowane fanni ciki
har da sojojin kasar nan.

Babangida ya yi kira ga Tinubu ya zama shugaban kasa ga dukkan ‘yan Nijeriya a daidai lokacin da ya karbi ragamar shugabancin kasar nan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *