Darakta-Janar ta hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa NAFDAC, Farfesa Mojisola Adeyeye tace sama da kaso 70 cikin 100 naMkayan abincin da ake fitarwa daga Najeriya ana ƙin karbar su a kasashen waje.
Farfesa Adeyeye ta bayyana hakan ne a wajen kaddamar da sabon ofishin hukumar NAFDAC na filin jirgin sama na Murtala Muhammed dake a jihar Legas.
A cikin wata sanarwa da mai bada shawara kan harkokin yada labarai a hukumar ta NAFDAC, Sayo Akintola, ya fitar,Adeyeye tace matsalar kin fitar da abinci daga Najeriya a wasu kasashen Turai da Amurka na iya zama tarihi nan bada jimawa ba, idan akayi hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu.
Hukumar da sauran hukumomin gwamnati a tashoshin jiragen ruwa sun karfafa ayyukan da suke domin tabbatar da komai ya tafiya yadda ya kamata.
Adeyeye tace,a halin da ake ciki na saukaka kasuwancin fitar da kayayyaki da aka kayyade daga kasarnan na cigaba da zama abin damuwa ga hukumar.
Ta kara da cewar ziyarar da hukumar ta NAFDAC ta keyi na fitar da kayayyakin dake cikin filin jirgin saman na kasa da kasa zai bayyana babban dalilin daya sa ake cigaba da kin amincewar hukumar.
Najeriya na fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje da dama, kuma kayan yawanci daga cikin wadanda takan samar ne.
A cewarta hukumar tana mayar da martani kan kalubalen da ake fuskanta ta hanyar hada kai da hukumomin da ke kula da tashoshin jiragen ruwa ta hanyar tabbatar da cewa kayayyakin sun cika ka’idojin kasashen da ake shigowa dasu da kuma wuraren da ake shigowa da su.