“Duk masu rike da mukaman siyasa u mika takardunsu na ajiye aiki daga yanzu zuwa ranar 26 ga Mayu, 2023”. — Ganduje

Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya umurci duk masu rike da mukaman siyasa dasu mika takardunsu na ajiye aiki daga yanzu zuwa ranar Juma’a 26 ga Mayu, 2023.

Masu rike da mukaman sun hada da kwamishinoni, masu bada shawara na musamman,da manyan jami’an gudanarwa na kamfanoni mallakar gwamnati, da babban mataimaki na musamman, da mataimaka na musamman, da kuma ma’aikatan hukumomin gwamnati.

A Wata sanarwa data fito daga babbar sakatariya a ofishin sakataren gwamnatin jihar, Bilkisu Shehu Maimota, ta umurce su dasu mika aiyukansu ga manyan sakatarori ko daraktocin gudanarwa na ma’aikatun gwamnati.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *