Buhari ya yi kira ga sojojin ruwan Najeriya dasu tabbatar da cewa suna bayar da tsaron da ya kamata

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga sojojin ruwan Najeriya da su tabbatar da cewa suna bayar da tsaron da ya Kamata, akan iyakokin Najeriya na ruwa.

Shugaban ya yi wannan kiran ne a wajen Wani taro da aka shiryawa shugaban kasar, mai taken “Tsarin Jirgin Ruwa don Ci gaban Kasa,” wanda Rundunar Sojojin Ruwa ta Najeriya ta shirya domin karrama shi.
Ya kuma yi nuni da cewa, rundunar sojin ruwan ta sanya dukkannin jiragen ruwa 20 da aka samu su yi amfani da su yadda ya kamata, kamar yadda ya bayyana a cikin nasarorin da aka samu a yakin da ake yi da satar albarkatun kasa, da yaki da muggan kwayoyi da kuma satar fasaha.

Ya bayyana cewa, fashin teku ya ragu matuka a cikin shekaru bakwai da suka gabata, wanda ya kai ga fitar da Najeriya daga jerin kasashen da ke fuskantar matsalar fashin teku a watan Maris na shekarar 2022.

Ya kuma ce yana da yakinin cewa zababben shugaban kasa, Bola Tinubu, zai dore da wa’adin gwamnatinsa wajen bai wa sojojin ruwan Najeriya tallafin da ya dace.

A jawabinsa na maraba, babban hafsan hafsoshin sojin ruwa, Vice Admiral Awwal Zubairu Gambo, ya bayyana cewa an shirya bitar ne domin karrama shugaban kasar, wanda a cewarsa, ya bayar da tallafin da ba a taba ganin irinsa ba ga sojojin ruwan Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *