Buhari ya amince da wasu kudirori da suka zama dokoki.

A daidai lokacin da yake shirye-shiryen barin mulki, shugaba Muhammadu Buhari ya amince da wasu kudirori da suka zama dokoki.

A jiya ne, Mai taimakawa shugaban kasa kan harkokin majalisar dattawa, Sanata Babajide Omoworare ya ce kudirorin takwas sun shiga dokokin kasa Hadimin shugaban na Najeriya yace shugaba Muhammadu Buhari ya amince da kudirorin da suka fito daga majalisa kamar yadda tsarin mulkin kasa ya ba shi iko.

A kudirorin majalisar tarayya da suka samu karbuwa a wajen shugaban kasa mai barin-gado akwai kudirin tsarin inganta rayuwar marasa galihu.

Baya ga kudirin kafa hukumar NSIP akwai kudirin Ilimin karatun sakandare da kudirin da ya bada damar kafa jami’ar kiwon lafiya a garin Azare dake jihar Bauchi.

Haka zalika dokar ta tabbatar da kafa wata jami’ar kiwon lafiya da ke Ila- Orangun a jihar Osun.

Kamar yadda rahoton da aka fitar ya nuna, sababbin dokokin da aka fito dasu za su inganta ilmin kwarewa a harkar akantanci da sanin akan aikin ofis.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *