Hukumar Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) ta ce za ta dauki Dala 100 daga cikin kudin guzurin maniyyata aikin Hajjin bana, domin biyan karin kudin kujera da kamfanonin jiragen da za su yi jigilar su suka yi.
Yakin da ake yi a Sudan ya sa kasar rufe sararin samaniyarta, don haka dole sai jiragen da za su dauki maniyyatan su bi sabuwar hanya da ta bi ta kasar Chadi da Habasha da Eretiyiya da Kamaru kafin isa kasar Saudiyya.
ِKafin barkewar yakin da ya sa aka rufe sararin samaniyyan Sudan, jiragen maniyyatan Najeriya kan tsallaka ne ta Chadi su shiga Sudan ne kadai kafin su isa Saudiyya.
A lokacin, hukumar ta ce za ta yi duk mai yiyuwa wajen ganin cewa ba a dora karin akan alhazan ba, amma kuma yanzu ta bayyana cewa za ta dauki karin da aka samu na kudin tikitin ne daga kudin guzurin maniyyata.
Shugaban Hukumar Jin dadin Alhazai ta Jihar Kano, Alhaji Muhammad Abba Dambatta, ya shaida wa ‘yan jarida cewa an rage karin kudin tikitn daga Dala 250 zuwa Dala 116, wanda kuma za a cire Dala 100 a guzurin alhazai, ita Hukumar NAHCON ta hukumomin jin dadin alhazai na jihohi za su dauki nauyin biyan Dala 15 a tsakaninsu.