“‘Yan sandan Kano sun mika wama’aikatar shari’a rahoton zargin kisa da ake zargin Alhassan Doguwa da aikatawa”. — Babban lauyan Kano

Babban Lauyan Jihar Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Musa Abdullahi Lawan ya tabbatar da
cewa rundunar ‘yan sandan jihar ta mika wa ma’aikatar shari’a ta jihar Kano rahoton zargin kisa da ake zargin Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Wakilai, Alhassan Ado Doguwa da aikatawa.

Da yake jawabi ga manema labarai a ofishinsa a ranar Juma’a, jim kadan bayan ya karbi takardar
bayanan, babban lauyan ya ce kwamishinan ‘yan sandan Jihar Kano ya mika takardar ga ma’aikatar da misalin karfe 12:45 na ranar jumaa .

Tun a baya Kwamishinan Shari’ah a Jahar Kano ya sanar cewa ma’aikatar ta mayar da rahoton ga
‘yan sanda don ci gaba da bincike, inda ta nemi karin bayani kan zargin da ake yi wa Doguwa don
gurfanar da shi a gaban Kotu.

Daga cikin bayanan da ma’aikatar ta nema har da hoton gawarwakin da aka kashe da bayanan
shaidu da bindigar da aka kwato da sauran abubuwan da ake zargin an yi amfani da su wajen
aikata laifukan.

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta kama Doguwa tare da gurfanar da shi tare da wasu bisa
laifin hada baki da kuma kisan kai, wanda ya saba wa sashe na 97, 114, 221,247 da 336 na kundin
final kod.

Dan sanda mai shigar da kara ya shaida wa kotun cewa Doguwa ya aikata laifin ne a ranar 26 ga
watan Fabrairu a Karamar Hukumar Tudun Wada anan Jihar Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *