‘Yan Majalisa sun musanta karɓar dala miliyan 15 daga gwamnati kafin su amince da sauya fasalin bashin nairatiriliyan 22 da ta karɓa

‘Yan Majalisar Wakilan Najeriya sun musanta zargin karɓar kuɗi dala miliyan 15 daga
gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari kafin su amince da buƙatar sauya fasalin bashin naira
tiriliyan 22 da ta karɓa daga Babban Bankin Najeriya (CBN).

Majalisar ta bayyana zargin da “maras tushe wanda kuma ba shi da makama” cikin wata
sanarwa da mai magana da yawunta, Benjamin Kalu, ya fitar ranar Juma’a.

Ya ce sai da suka tattaunawa da ɓangaren zartarwa da kuma tsettsefe buƙatar kafin su
amince.

Benjamin Kalu ya ce Idan ba a manta ba, Majalisa ta dakatar da buƙatar na wani lokaci don saboda
shawarar da wasu kwamatoci suka bayar ta gudanar da cikakken nazari game da aikin tallafa
wa al’umma da gwamnatin ta ce za ta yi da kuɗin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *